ABNA24 : Mahukuntan kasar sun ce za’a canza wa ‘yan gudun hijirar matsugunni.
Kimanin ‘yan gudun hijirar Mali 20,000 ne za a canza wa wurin zama daga sansanin na Intikane da ke yankin Tillia a jihar Tawa kusa da iyaka da Mali, zuwa wani gari mai suna Akadany da ke cikin jihar Maradi a tsakiyar kasar.
Tuni dai aka dakatar da ayyukan jinkai ga ‘yan gudun hijirar kamar dai yadda mahukunta a yankin suka tabbatar.
Gwamnatin Nijar ta ce, ta yanke wannan shawara ce bayan tattaunawa da jami’an Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR.
342/